Wannan sanarwar ta fito ne daga babbar mai shari'a ta kasar
Wani dan-jarida mai bincike Anas Aremeyaw ne dai ya dauki hotunan bidiyon alkalan a lokacin da ake zargin suna karbar hancin.
Dan jaridan ya ce yana da faifan bidiyo na kusan sa'oi 500 a matsayin hujja na abin da alkalan suka aikata, wanda aka gabatar wa Alkalin Alkalan kasar.
Tun daga wancan lokacin aka kafa kwamitin bincike.
Kwamitin binciken yana ci gaba da binciken sauran alkalan da ake zargi. 289